Isa ga babban shafi

Harin 'yan aware ya tilasta 'yan Kamaru fiye da 500 tsallakawa Najeriya

Fiye da ‘yan gudun hijirar Kamaru 500 ne daga kudu maso yammacinn kasar suka samu matsugunai yanzu haka a jihar Rivers ta Najeriya bayan wani mummunan harin ‘yan aware akan iyakar kasashen biyu jiya litinin da ya kai ga kisan tarin fararen hula.

Wasu 'yan gudun hijirar Kamaru da suka tsallaka Chadi cikin watan Disamban bara saboda hare-haren 'yan aware.
Wasu 'yan gudun hijirar Kamaru da suka tsallaka Chadi cikin watan Disamban bara saboda hare-haren 'yan aware. AFP - DJIMET WICHE
Talla

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Cross River da ke kudancin Najeriya SEMA ta tabbatar da karbar ‘yan gudun hijirar fiye da 500 wadanda ta ce tuni suka samu matsuguni a karamar hukumar Boki ta jihar.

A wani taron manema labarai da SEMA ta gudanar a Calabar babban birnin Cross River, ta ce hare-haren mayaka masu yunkurin ballewa daga kamaru don kafa kasar Ambazonia na tilastawa tarin ‘yan Kamaru kaura musamman daga yankin na Bashu da ke kudu maso yammacin kasar.

Tsawon shekaru kenan Kamaru na fama hare-haren ‘yan aware na yankin masu amfani da turancin ingilishi wanda ya haddasa asarar dubban rayuka galibi jami’an tsaro.

Akalla mutane 20 dukkaninsu fararen hula ne suka mutu a harin na ‘yan aware kan al’ummar Bushu da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya a daren jiya litinin.

Shugaban hukumar ta SEMA Princewill Ayim y ace zuwa yanzu basu da tabbacin ko cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai ‘yan Najeriya, said ai ya ce hukumar da taimakon sauran hukumomin kasa da kasa da ke taimakawa ‘yan gudun hijira na aiki don kai dauki yankin na Bushi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.