Isa ga babban shafi

Za a samu karancin ruwan sama a gabashin Afrika - Masana

Kungiyoyin Agaji tare da masana yanayi da noma sun bayyana fargabar cewar ana iya fuskantar karancin ruwan sama tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwambar bana a kasashen Kenya da Somali da kuma Habasha, a daidai lokacin da ake fama da yunwa a yankin sakamakon rashin ruwan sama na kusan shekaru 4.

Karancin ruwan ka iya ta'azzara matsalar fari da yunwa.
Karancin ruwan ka iya ta'azzara matsalar fari da yunwa. AP - Michael Tewelde
Talla

Rahotan kungiyoyin wanda ya kunshi Majalisar Dinkin Duniya ya ce ba’a taba ganin irin wannan yanayi mai tada hankali ba a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Karancin ruwan sama ya haifar da fari da mutuwar dabbobi da kuma rashin abinci ga miliyoyin mutanen da ke wannan yankin, abin da ya tilasta wa wasu barin gidajensu.

Kungiyoyin sun ce, tuni wannan fari ya hallaka akalla dabbobi sama da miliyoyin 3 da rabi a kasashen Kenya da Habasha, inda mazauna yankunan suka dogara da kiwo, yayin da kowacce dabba guda daga cikin 3 da ke Somalia ta mutu tun daga tsakiyar shekarar 2021 saboda karancin ruwan saman.

Rahotan wanda ya ce yanzu haka mutane miliyan 16 da dubu 700 ke fama da yunwa mai tsanani a kasashen guda 3, ya ce adadin na iya karuwa zuwa miliyan 20 nan da watan Satumba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.