'Yan tawayen Chadi sun yi kira da a saki 'yan adawa da aka tsare
Kungiyoyin 'yan tawayen kasar Chadi sun yi kira da a gaggauta sako gungun 'yan adawar da aka kama a farkon wannan wata sakamakon zanga-zangar kin jinin Faransa.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin 'yan tawayen sun yi kira da a gaggauta sakinsu ba tare da wani sharadi ba a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.
A ranar litinin, da ta gabata hukumomin Chadi sun tuhumi wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa ta Wakit Tamma da laifin cin zarafin jama'a sakamakon zanga-zangar da suka shirya ranar 14 ga watan Mayu wanda ta kaiga tsare su.
An tsare kodinetan Wakit Tamma, Max Loalngar, kuma an gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Alhamis, saidai an dage sauraron shari’ar nasu har zuwa ranar 6 ga watan Yuni.
Zanga-zangar ta shafi Faransa ne, wadda masu fafutuka ke zargin tana goyon bayan gwamnatin mulkin soja a Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu