Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta sake afkawa gabashin Afirka ta Kudu

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a Afirka ta Kudu, ya sake haifar da ambaliyar da ta tilastawa mutane kusan 500 tserewa daga gidajensu a gabar tekun gabashin kasar, wata guda kacal bayan da ambaliyar ruwa mafi muni a kasar da ta kashe mutane sama da 400.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye yankin Chatsworth, da ke wajen birnin Durban a Afirka ta Kudu.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye yankin Chatsworth, da ke wajen birnin Durban a Afirka ta Kudu. AP
Talla

Jami’an agaji dai sun ce, ba a samu asarar rayuka ba, sai dai hasarar dimbin dukiya, musamman a Durban, babban birnin lardin KwaZulu-Natal.

A karshen watan Afrilu, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutane 435 sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa, inda wadanda suka tsira daga Iftila’in suka shafe kusan makonni biyu ba tare da ruwan sha ba.

A cikin watan Afrilu, gamayyar kungiyoyin masu fafutukar yaki da matsalar sauyin yanayi sun garzaya kotu inda suka yi shigar da kara kan shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da wasu fitattun ministocinsa, bisa zarginsu da yin sakacin rashin daukar kwararan matakan magance matsalar ta sauyin yanayi a wasu sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.