Isa ga babban shafi

An kai harin ta'addanci fiye da dubu 5 cikin shekaru 3 a yammacin Afrika

Manyan hafsoshin tsaron kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS sun fara taron kwanaki 2 a kasar Ghana domin nazari akan matsalolin tsaron da suka addabi yankin da kuma yadda zasu hada kai domin tinkarar su.

Babban hafsan tsaron Najeriya, Major Janar Lucky Irabo.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Major Janar Lucky Irabo. Twitter@ Bashir Ahmad
Talla

Najeriya da Nijar da Mali da Burkina Faso na daga cikin kasashe 15 dake cikin kungiyar dake fama da matsalar tsaron dake da nasaba da ayyukan ta’addanci, yayin da kasashen Ghana da Jamhuriyar Benin da Cote d’Ivoire ke fargabar fantsamar tashin hankalin zuwa kasashensu.

Ministan tsaron Ghana Dominic Nitiwul ya bayyana cewar matsalar tsaro daga kungiyoyin dake dauke da makamai da masu aikata manyan laifuffuka na karuwa a yankin.

Nitiwul ya bukaci musayar labaran asiri a tsakanin jami’an tsaron domin tinkarar ayyukan wadannan bata gari wadanda ke jefa rayuwar jama’a cikin hadari.

Ministan yace a matsayin su na kwararu ya dace suyi watsi da batun maganar al’ada da addini da kasa wajen hada kai a tsakanin su da zummar samun nasara.

Nitiwul ya ce a cikin shekaru 3 da suka gabata, Yankin ya fuskanci sama da hare-haren ta’addanci 5,300 abinda ya yi sanadiyar hallaka mutane kusan 16,000, yayin da a cikin watanni 3 na wannan shekarar aka samu hare-hare sama da 840.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.