Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Kasar Guinea ta tsare wasu makusantan Conde bisa zargin cin hanci

Sojojin da ke mulkin Guinea Conakry, sun tsare wasu tsoffin jiga jigan 'yan siyasar kasar biyu bisa zargin su da cin hanci da rashawa.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea Kanal Mamadi Doumbouya,a birnin Conakry, 10 ga Satumban, 2021.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea Kanal Mamadi Doumbouya,a birnin Conakry, 10 ga Satumban, 2021. REUTERS - SALIOU SAMB
Talla

Wannan na zuwa a yayin da sojojin suka kara kaimi wajen murkushe fitattun ‘yan siyasar kasar da ke da kusanci da hambararren shugaban kasar Alpha Conde.

Sojojin da suka yi juyin mulki a cikin watan Satumba sun zargi gwamnatin Conde da kasancewa dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa da kuma mulkin-kama karya.

Wadanda aka tsaren a baya-bayan nan sun hada da tsohon kakakin majalisa da kuma tsohon shugaban hukumar zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.