Isa ga babban shafi

Kwame Nkrumah ya cika shekaru 50 da rasuwa

Yau ake cika shekaru 50 da rasuwar shugaban Ghana na farko Dakta Kwame Nkrumah, wanda aka yi wa juyin mulki a shekarar 1966.

Shugaban kasar Ghana na farko Kwame Nkrumah, yayin gabatar da jawabi a fadar White House ta Amurka kan halin da kasashen Afirka ke ciki , 8 ga Maris,1961.
Shugaban kasar Ghana na farko Kwame Nkrumah, yayin gabatar da jawabi a fadar White House ta Amurka kan halin da kasashen Afirka ke ciki , 8 ga Maris,1961. © AP/Archive
Talla

Al’ummar Ghana da ma nahiyar Afirka na tunawa da gwarzon shugaban saboda rawar da ya taka wajen neman ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka da kuma manufofinsa na neman cigaban bakar fata.

Nkrumah ya rasu ne a ranar 27 ga Afrilu na shekarar 1972 yana da shekaru 62, yayin da yake fama da cutar daji, inda ya rasu a Bucharest babban birnin kasar Romania.

Kwame Nkrumah.
Kwame Nkrumah. Terry Fincher/Express/Getty Images

An hambarar da gwamnatin Dakta Kwame Nkrumah ne a wani juyin mulki da Kanar Emmanuel Kwasi Kotoka ya jagoranta a ranar 24 ga Fabrairu, na shekarar 1966, a lokacin da shugaban ke gudanar da ziyarar aiki a kasar waje.

Tun bayan juyin mulkin da aka yi masa ne kuma, tsohon shugaban  na Ghana ya koma kasar Guinea da zama, inda ya kasance Fira Minista na farko a kasar.

Marigayi Kwame Nkrumah yana cikin mutane 6 wadanda suka kulla yarjejeniyar United Gold Coast Convention, wadda ta haifar kafuwar jam’iyyarsu ta UGCC a takaice da tayi fafutukar kwatarwa kasar Ghana ‘yanci daga mulkin mallakar Birtaniya, bayan yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.