Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kammala lalata rayuwar 'yan Najeriya - Bishop Kukah

Babban Limamin mabiya darikar Katolika dake Sokoto a Najeriya, Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala lalata duk wani bangare na rayuwar jama’ar kasar a karkashin gwamnatin sa tare da baiwa cin hanci da rashawa damar habaka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/@BashirAhmad
Talla

Yayin da yake gabatar da sakon bikin Easter a mujami’ar sa, Kukah yace duk wani bangaren rayuwar jama’ar Najeriya ya lalace, yayin da kasar ta zama sashen gobe da nisa na asibiti dauke da tarin marasa lafiya.

Limamin yace zukatan ‘Yan Najeriya tare da iyalansu da gidajen su da Mujami’u da Masallatai da kayan more rayuwa duk sun ruguje a karkashin gwamnatin Buhari.

Babban Limamin mabiya darikar Katolika dake Sokoto a Najeriya, Bishop Mathew Hassan Kukah tare da Fafurama
Babban Limamin mabiya darikar Katolika dake Sokoto a Najeriya, Bishop Mathew Hassan Kukah tare da Fafurama saharareporters

Kukah yace harkokin ilimin kasar ya ruguje tare da rayuwa da makomar ’yaran kasar kamar yadda bangaren siyasa da tattalin arziki da makamashi da al’ummomi da hanyoyin mota da na jiragen kasa suka ruge inda babu abinda ke rayuwa yadda ake bukata da ya wuce cin hanci da rashawa.

‘Yan Najeriya basa iya gane kasar su

Limamin yace yau ‘Yan Najeriya basa iya gane kasar su saboda yadda ta fita daga cikin hayyacin ta sakamakon matsalolin da suka mamaye ta a karkashin gwamnatin Buhari.

Kukah yace lura da irin wadannan dimbin matsalolin da suka addabi Najeriya wasu ‘Yan kasar na tambayar ko masu rike da madafun ikon a basa ji ko gani ko dandanar irin yanayin da jama’ar kasar suka samu kan su ne ko kuma suna nuna halin ko-in-kula ne domin babu abinda ya dame su.

Matakin sake dawo da kimar kasar

Limamin yace babban kalubalen dake gaban jam’ar Najeriya ayau itace yadda za’a fara daukar matakin sake dawo da kimar kasar da fatar mutane zasu rayu har zuwa lokacin zaben shekara mai zuwa da kuma sanya ido akan abinda zai biyo baya domin fuskantar matsalolin da suka addabi kasar ta hanyar gina halayen jama’a da kuma son kasa.

Kukah ya bukaci shugabannin addinai da su tashi tsaye cikin gaggawa domin ceto Najeriya daga halin da ta samu kanta, musamman ganin yadda yanzu ake samun miliyoyin mutane a cikin kasar da duniya baki daya dake barin addinin Krista da Musulunci domin zama marasa addinai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.