Isa ga babban shafi

An saki tsohon shugaban Burkina Faso daga daurin talala

Sojojin Burkina Faso sun saki tsohon shugaban kasar Roch Kabore, wanda ke tsare a hannunsu tun bayan juyin mulkin da suka yi masa a watan Janairun da ya gabata.

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré.
Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré. JACQUES DEMARTHON / AFP
Talla

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Fason ta ce an baiwa Kabore damar komawa gidansa dake Ougadougou babban birnin kasar a ranar Laraba, inda aka sanya matakan tsaro don "tabbatar da tsaron lafiyarsa".

A watan da ya gabata, shugabannin kasashen yammacin Afirka suka bukaci gwamnatin sojin ta saki tsohon shugaban kasar tare da gaggauta tsayar da lokaci na "mafi karbuwa" na shirya zabe domin komawa ga tsarin mulkin dimokuradiyya, sabanin lokacin da suka tsara na shafe watanni 36 suna rikon kwarya.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso na cigaba da yin watsi da matsin lamba daga kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, kan neman yin murabus daga mulki cikin kasa da shekaru uku, tana mai cewa abin da ta sa gaba shi ne magance matsalar rashin tsaro a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.