Isa ga babban shafi
Mali

Tsohon Franministan Mali Boubèye Maïga ya rasu a hannun sojoji

Tsohon Franministan Mali Soumeylou Boubèye Maïga da hukumomin ke tsare da shi kan rufta ciki da dukiyar kasa, ya rasu da tsakar ranar yau a wani asibiti dake Bamako yana da shekaru 67 a duniya.

Tsohon Franministan Mali Soumeylou Boubèye Maïga a watan Maris shekarar 2019
Tsohon Franministan Mali Soumeylou Boubèye Maïga a watan Maris shekarar 2019 © wikimedia.org
Talla

 ‘Yan uwa da iyalan tsohon Franministan suka tabbatarwa RFI rasuwarsa da safiyar wannan Litinin.

Tun cikin watan Agusta aka tsare Soumeylou Boubeye Maiga, wanda tsohon franminitsa ne tsakanin watan Dismambar shekarar 2017 zuwa Afrilun 2019, bisa zargin almundahana a wani bangare na bincike kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnati keyi, wanda ke da alaka da kwangilar sayan kayayyakin aikin soja.

Watanni uku da suka gabata aka kwantar da tsohon franminitsan a gadon asibi a Bamako sakamakon tabarbarewar yanayin lafiyarsa, wanda aka alakanta da halin da ya fuskanci kansa a inda ake tsare da shi.

Likitoci sun bukaci fitar da shi kasashen waje domin samun kulawar kiwon lafiya, amma hukumomin rikon kwarya ta sojin kasar sukayi biris da bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.