SENEGAL - TSARO
'Yan kasar Senegal dubu 6 sun tsere wa rikicin 'yan aware zuwa Gambia
Hukumomin Gambiya suka ce yanzu haka sama da ‘yan kasar Senegal dubu 6 suka nemi mafaka bayan da suka tserewa tashe tashen hankula na tsawon mako guda tsakanin sojoji da ‘yan tawaye a Casamance, da ke kudancin kasar Senegal.
Wallafawa ranar:
Talla
Rundunar sojin Senegal ta sanar da cewa a ranar 13 ga watan Maris ta kaddamar da farmaki kan 'yan tawaye a birnin Casamance mai makwabtaka da Gambia.
Mutanen da ke tserewa tashin hankalin da aka gano tun ranar 13 ga Maris sun kai 6,350, in ji Hukumar Kula da bala’o’i ta kasar Gambiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu