Algeria ta janye jakadanta na Spain
Algeria ta umurci jakadanta na kasar Spain ya dawo gida biyo bayan shawarar kasar ta bada goyon baya ga shirin da Morocco ke yi na bada ikon cin gashin kai ga yankin Arewacin Sahara da ake rikici a kai a karkashin kasarta.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta yi tir da Spain, wadda kafin yanzu bata nuna goyon baya ga kowane bangare ba a kan rikicin da aka shafe gwamman shekaru ana yi tsakanin Morocco da Algeria a kan yankin na Arewacin sahara.
A ranar Juma’a ce ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares ya bayyana matakin gwamnatin kasarsa na goyon bayan Morocco a kan bada kwarya kwaryar ikon cin gashin kai ga Arewacin Saharar a karkashinta
Algeria ta bayyana kaduwarta a game da sauyin manufa da Spain ta yi, ta wajen bada goyon baya ga Morocco a kan wannan rashin jituwa tsakanin kasashen biyu na yankin arewacin Afrika.
Kungiyar Polisario da ke fafutukar neman yancin arewacin Saharar ta mayar da martini cikin fushi ga sanarwar Spain, tana mai kira da a matsa mata lamba har sai ta sauya ra’ayinta.
Kungiyar ta yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da majalisar dinkin duniya ta taimaka aka cimma a shekarar 1991, wadda ya tanadi cewa za a gudanar da zaben raba gardama a kan idonta, a game da batun samun yancin kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu