Isa ga babban shafi

Bakin haure 70 sun mutu a tekun Libya

Kimanin bakin haure 70 ne ake fargabar sun mutu bayan sun bace a gabar tekun Libya tun cikin watan Fabairun da ya gabata, kamar yadda Hukumar Kula da Kauren Baki ta Duniya ta bayyana.

Ana yawan samun asarar rayukan baki-haure a teku a kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai.
Ana yawan samun asarar rayukan baki-haure a teku a kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai. © REUTERS - STEPHANE MAHE
Talla

Hukumar Kauren Bakin ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kawo yanzu an gano gawarwakin bakin hauren 22 bayan kwalekwalensu ya kifa a teku tun a ranar 27 ga watan Fabairu da kuma 12 ga watan Maris, yayin da ake ci gaba da neman 47.

Shugaban Hukumar ta IOM a Libya Federoico Soda ya ce, ya kadu matuka da yadda ake ci gaba da samun asarar rayukan  bakin haure a tsakiyar tekun Mediterranean, yayin da hukumomi suka gaza daukar matakan yaki da matsalar.

Jami’in ya yi kira da a dauki kwakkwaran mataki na rage asarar rayuka ta hanyar kara kaimi wajen lalubo mutane tare da ceto su ko kuma tabbatar da saukarsu lafiya daga jirgin ruwa.

Ana kallon hanyar tsakiyar tekun Mediterranean a matsayin mafi hatsari a duniya ga bakin haure masu kokarin tsallakawa zuwa Turai, amma duk da haka wasu na daukar kasadar ratsawa ta hanyar.

Sama da bakin haure dubu 123 ne suka isa kasar Italiya daga Libya da kuma Tunisia a bara kadai, adadin da ya zarta  dubu 95 da aka gani a shekara ta 2020 kamar yadda alkaluman hukumar kula da ‘ya gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.