Mahaukaciyar Iska Da Ruwan Sama Sun tsugunar da Harkoki a Mauritius
A kasar Mauritius dubban gidaje suka rasa hasken wutan lantarki bayan da mahaukaciyar iska da ruwan sama suka ratsa kasar.
Wallafawa ranar:
Mahaukaciyar iska da ruwan saman da suka rika gudun kilomita 130 cikin sa’a guda sun yi barnar gaske a babban birnin kasar Port Louis.
Wannan mahaukaciyar iska da goguwa da ruwan sama sun tsaida dukkan harkokin yau da kullum a fadin kasar.
Hukumomi na cewa gidaje akalla 7,500 babu hasken wutan lantarki bayan da iska da itatuwa suka karya turakun wayoyin lantarki.
Kazalika wayoyin sadarwa sun fuskanci matsala sakamakon iska.
A shekara ta 2007 mutane biyu suka rasa rayukansu sakamakon irin wannan mahaukaciyar iska da ruwan sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu