Isa ga babban shafi
SENEGAL - TSARO

'Yan tawaye sun kashe sojojin Senegal 4 tare da garkuwa da 7

Majiyar tsaro a Senegal  ta sanar da mutuwar sojin kasar hudu a hannun ‘yan tawaye, baya ga yin garkuwa da wasu 7 sakamakon rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu cikin makon da ya gabata a kan iyakar kasar da Gambia.

Sojojin Senegal yayin sintiri a garin Barra.
Sojojin Senegal yayin sintiri a garin Barra. Carl de Souza/AFP
Talla

Sanarwar na cewa a ranar 24 ga watan Janairu da ya kare, daidai lokacin da rikici ya kaure tsakanin jami’an sojin Senegal da 'yan tawayen MFDC, sojoji 3 suka mutu, sannan kwanaki  bayan faruwar lamarin na hudun ya kwanta dama bayan jinyar da ya yi daga raunin da ya samu a rikicin.

Majiyar sojin Senegal ta kuma ce a halin yanzu ‘yan tawayen MFDC na rike da jami’an sojinta 7, kuma dukanninsu na cikin koshin lafiya.

Kungiyar ta MFDC ke da alhakin rikicin da ya barke a  shekarar 1982 a yankin kudancin Senegal, wanda yayi sanadiyar hasarar dubban rayuka.

A sanarwar farko da majiyar ta fitar, ta ce sojinta biyu aka kashe tare da tsare wasu 9, kuma babu wanda ya bace, toh saidai bayan tabbatar da sahihin adadin wadanda lamarin ya rutsa da su, ta sake fitar da sabuwar sanarwar dake bayyana halin da ake ciki a yanzu.

Wadannan Sojin dai na daga cikin jami’an da kungiyar ECOWAS ta tura Gambia domin wanzar da zaman lafiya a shekarar 2017, daidai lokacin da tsohon shugaban Kasar Yahya Jameh yaki sauka daga kan mulki duk kuwa da cewa ya fadi zabe, jami’an da aka fi sani da suna ECOMIG

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.