Kasashen duniya na dakon ranar zaben Libya
Amurka da wasu manyan kasashen Turai sun bukaci Libya da ta gaggauta tsayar da sabuwar ranar gudanar da zaben shugabancin kasar da aka jinkirta.
Wallafawa ranar:
A cikin wata sanarwar hadin-guiwa da kasashen suka fitar, sun roki jagororin Libya da su fitar da jerin sunayen karshe na ‘yan takarar shugabancin kasar.
Tun da fari, hukumomin da ke sanya ido kan zaben na Libya sun ce, mawuyaci ne a gudanar da zaben a jiya Juma’a kamar yadda aka tsara da farko.
Yanzu haka masu shirya zaben na duba yiwuwar gudanar da shi a ranar 24 ga watan Janairu mai zuwa, amma ana ganin da wahala sauran bangarorin kasar su amince da wannan rana.
Ana sa ran wannan zaben zai bude sabon babin rayuwa ga kasar ta Libya wadda ta kwashe tsawon shekaru tana fama da rikice-rikice.
Rikicin ya samo asali ne tun bayan da aka kashe tsohon shugaban kasar Mo’ammar Gaddafi a shekarar 2011 a wani juyin mulki da aka yi masa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu