Isa ga babban shafi
Algeria-IMF

Algeria za ta janye tallafin kayakin masarufi bayan shawarar IMF

Gwamnatin Algeria ta sanar da shirin janye tallafin kayakin masarufi sakamakon raguwar kudaden shigarta daga bangaren makamashi a wani yunkuri na kaucewa fuskantar gibi a kasafin kudin kasar.

Tsawon shekaru Algeria na sanyawa al'ummarta tallafin a kayakin masarufi kama daga madara da burodi har zuwa ga man fetur da lantarki.
Tsawon shekaru Algeria na sanyawa al'ummarta tallafin a kayakin masarufi kama daga madara da burodi har zuwa ga man fetur da lantarki. Ryad KRAMDI AFP
Talla

Matakin cire tallafin na Algeria ya biyo bayan bukatar hakan daga asusun bada lamuni na Duniya IMF da ke ganin ta wannan hanyar ne kadai kasar za ta ceto kanta daga matsalar tattalin arziki.

Tuni dai masana tattalin arziki suka goyi bayan matakin gwamnatin sai dai akwai fargaba yiwuwar janye tallafin ya haddasa tsadar rayuwa tare da tunzura matalauta da ke dogara da tallafin wajen tafiyar da rayuwarsu yau da kullum.

Kasar ta arewacin Afrika tattalin arzikinta ya dogara ne da albarkatun man fetur da iskar gas yayinda ta shafe shekaru wajen sanya tallafi a kusan ilahirin kayakin masarufin da al’ummar kasar ke siya baya ga man fetur da lantarki gabanin fuskantar matsalar tattalin arziki a bana.

A watan jiya ne asusun bada lamuni na IMF ya bukaci Algeria ta janye tallafin don ceto tattalin arzikinta wanda ya fuskanci koma baya tun bayan annobar covid-19.

Sai dai marasa karfi na ci gaba da koke kana bin da matakin zai haifar dai dai lokacin da rayuwa ke kara tsada.

A makon jiya, majalisar wakilan kasar ta tafka muhawara kan matakin wanda ya samu rinjayen kuri’a.

Kowanne lokaci daga yanzu ne Algeria za ta fara aiwatar da kudirin wanda zai kawo karshen biliyoyin dalolin da ta ke kashewa kowacce shekara a sanya tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.