Isa ga babban shafi
AFIRKA-KORONA

OXFAM da DFI sun yi gargadi akan tattalin arzikin Afirka ta Yamma

Kungiyar Agaji ta Oxfam da ta DFI sun yi gargadin cewar gwamnatocin kasashen Afirka ta Yamma na iya jefa kasashen su cikin mummunar matsalar tattalin arziki sakamakon rage kashe kudade sakamakon illar annobar korona.

Alamar kungiyar agaji ta Oxfam
Alamar kungiyar agaji ta Oxfam Andy Buchanan AFP/File
Talla

Rahotan da kungiyoyin biyu suka gabatar yace kasashe 14 daga cikin 16 dake Yankin Afirka ta Yamma sun shirya zabtare kasafin kudaden su saboda illar annobar, inda suka basu shawarar mayar da hankali wajen kara yawan harajin da ake dorawa attajirai maimakon zabtare kasafin kudin da zai taimakawa jama’ar kasashen su.

Rahotan da kungiyoyin suka gabatar, yace zabtare kasafin kudin zai haifar da rashin daidaito a tsakanin jama’a da kuma jefa wasu kasashe cikin matsaloli, musamman ganin yadda basussuka suka musu katutu.

Maganin rigakafin Moderna
Maganin rigakafin Moderna JOEL SAGET AFP

Kungiyoyin sun ce annobar da aka gani na iya haifar da mummunar matsalar da ba’a taba ganin irin ta ba da kuma jefa miliyoyin jama’a cikin kangin talauci.

Rahotan kungiyar yace matsalar zata fi yin illa ga mata, saboda yadda suka fi ayyuka wadanda ban a hukuma ko  kamfanoni ba, ko kuma inda za’a biya su albashi.

Kungiyoyin sun ce alkaluma sun nuna cewar, Yankin Afirka ta Yamma bai fuskanci illar annobar korona kamar yadda wasu yankuna suka gani ba, amma kuma matsalar annobar tayi illa sosai akan tattalin arzikin su.

Rahotan yace kasashen Yankin sun yi asarar da ta kai kusan Dala biliyan 49 bara, abinda Daraktar kula da Yankin na kungiyar Oxfam Assalama Dawalak Sidi ta bayyana shi a matsayin koma baya.

Wasu daga cikin kasashen dake Afirka ta Yamma na fama da tsananin talauci, yayin da irin su Mali da Nijar kuma ke fama da ‘Yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.