Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Hadarin kwale-kwale ya hallaka sama da mutum 100 a Jamhuriyar Kwango

Hukumomin Jamhuriyar Demokradiyar Kwango suka ce sama da mutane 100 ne suka mutu ko suka bace  a ruwan kasar bayan da kwale -kwale tara da ke hade da juna ya nutse a wannan makon. wanda shi ne hadari na baya -bayan nan a jerin hadurran ruwa da ake samu a kasar da al’ummar ta yawaitan amfani da jiragen ruwa.

Yadda ake hada-hadar daukar mutane da kwale-kwale a jamhuriyar Demokradiyar Kwango.
Yadda ake hada-hadar daukar mutane da kwale-kwale a jamhuriyar Demokradiyar Kwango. Photo Monusco/Alain Wandimoyi
Talla

Ana kwatanta jiragen ruwan Kwango da rashin inganci da kuma daukar kaya mara kima yayin da suke hada-hada a daya daga cikin manyan kogunan Afirka.

An gano gawarwakin mutane sittin bayan nutsewar kwale-kwalen a cikin daren Litinin zuwa Talata, yayin da ake kyautata zaton wasu Karin 60 sun bace, kamar yadda Nestor Magbado, kakakin gwamnan lardin Mongala da ke arewa maso yammacin kasar ya shaida wa AFP.

Jami’in yace an samu ceto mutane 39 da suka tsira da rayuwarsu.

Magbado yace, jirgin ruwan kwalekwale ne na katako irin na da kuma su tara aka daure su wuri guda, kuma ana kiransa Pirogue.

Ya kara da cewa mai yiyuwa hatsarin ya faru ne saboda “cunkoson mutane da rashin kyawun yanayi” cikin dare.

Kakakin gwamnatin lardin yace kwale-kwalen na dauke bangarorin al’umma daban-daban, kama daga matafiya da kuma daliban da ke tafiya Bumba babban birnin lardin.

Yace, yanzu haka ana ci gaba da aikin ceto, amma babu fatan samun masu sauran nunfashi, inda ya kara da ceto masu ikin ceto na fuskantar rashin kayan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.