Isa ga babban shafi
Morocco

Masu ra'ayin Islama sun rasa kujerunsu a zaben Morocco

Jam’iyyar masu ra’ayin islama ta rasa mafi yawan kujerun da take da su a zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar a jiya Laraba a kasar Morocco.

Shugaban Jam'iyyar PJD ta Morocco, Saad-Eddine El Othmani
Shugaban Jam'iyyar PJD ta Morocco, Saad-Eddine El Othmani FADEL SENNA AFP/File
Talla

Sanarwar da Ma’aikatar Cikin Gidan kasar ta fitar ta nuna cewa jam’iyyar PJD ta masu ra’ayin islama ta samu kujeru 12 ne a maimakon 125 da take da su a zauren majalisar a can baya.

Jam’iyyun hamayya da suka samu nasara sun hada da RNI wadda ta kwashe kujeru 97 da kuma PAM wadda ta samu kujeru 82, sai kuma jam’iyyar Istiqlal da ta samu kujeru 78 daga cikin 395 da ake da su a majalisar dokokin.

Wannan rashin nasarar da PJD ta yi, ya bada mamaki, amma duk da haka wasu masharhanta kan lamurran siyasa na ganin cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da  jagoranci.

Jam’iyyar ta masu ra’ayin Islama ta dare kan karagar mulki ne a shekarar 2011, bayan juyin-juyan halin da aka gani a kasashen Larabawa da ke yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yankin Arewacin Afrika.

Ana sa ran fitar da cikakken sakamakon zaben wani lokaci a yau Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.