Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Tsohon ministan lafiyar Congo ya shiga hannu saboda wawurshe kudin korona

Hukumonin Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun tsare tsohon ministan lafiyar kasar Eteni Longondo kan zargin karkatar da kudaden da aka ware don yaki da cutar coronavirus.

Tsohon ministan lafiyar jamhuriyar Demokradiyar Congo Eteni Longondo, yayin wani taron manema labarai a Kinshasa.
Tsohon ministan lafiyar jamhuriyar Demokradiyar Congo Eteni Longondo, yayin wani taron manema labarai a Kinshasa. © RFI / Pascal Mulegwa
Talla

Majajiyar gwamnati tace, an tsare tsohon ministan ne karkashin sammacin kama shi ta kotu da bayar a maraicen Jumma’a "bayan bincike na dogon lokaci.

Tsohon ministan lafiya, wanda ke kan mukaminsa har zuwa watan Afrilu, an kai shi gidan yarin Makala da ke Kinshasa babban birnin kasar, a cewar wani jami'in gidan yarin da ya bukaci sakaya sunansa.

Longondo, wanda ya jagoranci ma'aikatar lafiya tun daga watan Satumbar 2019, ana tuhumar sa da "almubazzaranci da dukiyar jama'a da aka ware don mayar da martani" kan cutar ta Covid-19, in ji Kungiyar Adalci ta Congo (ACAJ) a shafin Twitter.

Longondo ya musanta duk wata zargin yana mai cewa kudaden da ake magana a kai, wadanda ake kyautata zaton sun haura dala miliyan 7, “ana kan tantance su” a lokacin binciken.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.