Isa ga babban shafi
Algeria-Morocco

Dalilan da suka janyo katsewar hulda tsakanin Algeria da Morocco

Algeria ta katse huldar diflomasiya da makwabciyarta Morocco da suka dade suna hararar juna a yankin arewacin Afrika, yayin da ake kallon Isra'ila a matsayin wadda ta sabbaba sukurkucewar alakar kasashen biyu a baya-bayan nan.

Tutocin Morocco da Algeria
Tutocin Morocco da Algeria AFP - ABDELHAK SENNA
Talla

Tun ba yau ba, Algeria ke takun-saka da Morocco musamman saboda wani yanki da ke yammacin Sahara da Morocco ke kallo a matsayin mallakinta, amma Algeria ke goyo baya ga ‘yan awaren yankin na Polisario masu fafatukar ballewa.

A shekara da ta gabata ne, sukurkucewar dangantakarsu ta dauki sabon salo, lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya amince da mulkin Morocco a yankin na Polisario a matsayin tukuici ga gwamnatin Rabat wadda ita ma ta maido da huldarta da Isra’ila.

Wannan ne ya bai wa Morocco karfin guiwar kawo sojojin kasashen ketare zuwa yankin Maghreb kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Algeria, Ramtane Lamamra ya yi zargi.

Kazalika gwamnatin shugaba Joe Biden ta yanzu, ba ta nuna wata alamar cewa, za ta sauya matsayin da Trump  ya dauka a wancan lokaci ba kafin ya mika mulki.

Masharhanta irinsu Jalel Harchaoui na cibiyar Global Initiative, na ganin cewa, shurun da Biden ya yi na a matsayin gagarumin koma-baya ga Algeria, kasar da ta tuni rikice-rikice na cikin gida suka dabaibaye ta.

Algeria ta fusata lokacin da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Yair Lapid ya ziyarci Rabat a cikin wannan wata na Agusta, inda ya bayyana damuwarsa kan rawar da Algiers ke takawa a yankin arewacin Afrika tare da yaukaka alakarta da Iran.

Alakar kasashen biyu ta dada lalacewa ne a ‘yan kwanakin nan saboda wasu kalamai da suka fito daga bakin jakadan Morocco, Omar Hilale da ke nuna goyon baya ga yankin Kabylie mai neman ‘yancin cin gashin kai daga Algeria.

A dalilin wadannan kalamai na Hilale, Algeria ba ta yi wata-wata ba wajen janye jakadanta daga Morocco.

Kazalika lokacin da wutar daji ta mamaye arewacin Algeria a farkon wannan wata  tare da kashe mutane akalla 90, cikin gaggawa hukumomin kasar suka zargi kungiyar ‘yan kabilar Berber mai fafutukar neman ‘yancin kai a yankin na Berber, yayin da kuma Algeria ta zargi Morocco ta mara wa kabilar baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.