Isa ga babban shafi
Noma-Afrika

Manoman Afrika na asarar Dala biliyan 65 saboda kwari

Wasu kwari kuma tsutsotsi da aka bayyana cewa ayyukan dan adam ne ke haifar da su, na janyo wa manoman nahiyar Afirka asarar da ta kai Dala bilyan 65 a kowace shekara kamar dai yadda wani rahoto da aka fitar ya nuna.

Kwari na janyo wa manoman Afrika dimbin asara a kowacce shekara
Kwari na janyo wa manoman Afrika dimbin asara a kowacce shekara Money SHARMA AFP
Talla

Rahoton ya bayyana cewa, wasu nau’ukan tsirrai da kuma kwari ko kuma tsutsotsi, na haifar da mummunar illa ga amfanin gona, lamarin da ke zama babban kalubale ga nahiyar wadda ke kokarin wadatar da kanta da abinci.

Binciken ya dogara ne da wasu alkalumma da aka tattara daga kasashen Ghana, Kenya, Birtaniya da Switzerland, inda ya gano cewa a Afrika ne aka fi samu irin wadannan kwari masu lalata da amfanin gona.

Hakazalika masu binciken sun zanta da mutane sama da dubu daya ciki har da manoma, da masana aikin gona da kuma gwamnatoci wadanda suka bayyana yadda kwarin suka haifar masu da koma-baya tare raguwar samun kudaden shiga.

To sai dai masu binciken sun amince da cewa an samu kuskure a game da wani sakamako da suka fitar a baya, da ke cewa asarar ta kai ta Dala triliyan uku, inda a yanzu aka dawo da alkalumman zuwa Dala bilyan 65 a kowace shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.