Isa ga babban shafi
RIKICIN-KABILANCI

MDD tace Yan kasar Kamaru 10,000 sun tsere zuwa Chadi

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla Yan kasar Kamaru 10,000 akasarin su mata da yara ne suka gudu daga cikin kasar zuwa Chadi domin kaucewa tashin hankalin da akayi tsakanin masunta da makiyaya a wannan mako.

Shugaba Paul Biya
Shugaba Paul Biya Ludovic MARIN / AFP
Talla

Iris Blom, mataimakiyar Daraktar Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar tace mutanen na matukar bukatar abinci da matsuguni da kuma magunguna.

Rahotanni sun ce mutane 12 aka kashe yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin fadan da akayi tsakanin bangarorin biyu dake Jihar Arewa Mai Nisa.

Gwamnan Lardin Mijinyawa Bakari yace an samu rikicin ne sakamakon gina wata madatsar ruwa da Musulmi suka yi domin taimaka musu kamun kifi a yankin da Larabawa ko kuma Shuwa Arab makiyaya ke kiwon dabbobin su.

Ba’a cika samun fadar kabilanci a kasar Kamaru ba kamar yadda ake gani a kasashen Chadi da Najeriya, musamman abinda ya shafi manoma da makiyaya.

Gwamnan yace tuni aka tura jami’an tsaro domin magance rikicin da kuma tabbatar da cewar matsalar bata yadu ba.

Gwamnan Chari-Baguirmi Gayang Souare yace wasu daga cikin Yan gudun hijirar an basu matsuguni a gidaje, yayin da wasu kuma aka aje su a makarantu da mujami’u.

Jihar Arewa Mai Nisa ta Kamaru tana kuma fama da hare haren mayakan kungiyar boko haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.