Isa ga babban shafi
Kenya-Maita

Ina jin dadin shan jinin bil'adama- Wani maye

'Yan sandan kasar Kenya sun gabatar da wani matashin maye ga manema labarai bayan da ya yi ikirarin cewa ya kashe kananan yara akalla 10 ta hanyar tsotse jininsu.

Milimo Wanjala, mayen da ke shan jini kananan yara ya shiga hannun jami'an tsaro.
Milimo Wanjala, mayen da ke shan jini kananan yara ya shiga hannun jami'an tsaro. © lailasnews
Talla

Mutumin mai suna Masten Milimo Wanjala mai shekaru 20 a duniya, an kama shi ne ranar Laraba, biyo bayan gano gawarwarkin wasu kananan yara guda biyu a wata unguwa da ke wajen birnin Nairobi.

Lokacin da ake yi masa tambayoyi, Wanjala ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa ya kashe akalla mutane 10 ta hanyar tsotse masu jini, inda ya ci gaba da cewa sam ba ya nadama, saboda a cewarsa yana jin dadi a rayuwarsa idan ya tsotsi jinin bil’adama.

Rundunar ‘yan sanda ta ce mafi yawan wadanda Wanjala ya kashe yara ne ‘yan shekaru 5, 12 da kuma 13 a duniya.

A fitowarsu ta safiyar yau Alhamis, mafi yawan jaridun kasar Kenya sun wallafa hoton wannan mutum sanye da rigar kwallon kafa mai launin shudi sannan da alamun jini a jikinsa.

To sai dai ‘yan sandan sun ce, wani lokaci a baya, Masten Milimo Wanjala, ya bukaci mahaifan wani yaro da ya kamata su biya shi Shillings dubu 30 kudin Kenya, kimanin Dala 277 kafin daga bisani ya kashe shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.