Afrika ta yi asarar dala biliyan 8 a bangaren sufurun jirage cikin 2020- IATA
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa IATA, ta ce kamfanonin jiragen saman nahiyar Afirka sun yi asarar dala milyan dubu 7 da milyan 700 cikin shekarar da ta 2020 gabata.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta ce kamfanonin sun yi wannan asara ce sakamakon tsauraran matakai da kasashen duniya suka dauka don hana yaduwar annobar corona da ta tsananta a baran.
Daraktan hukumar da ke kula da nahiyar Afrika da gabas ta tsakiya Kami Alawadi ya ce akalla ma’aikata miliyan bakwai matsalar ta shafa kai tsaye sakamakon durkushewar manyan kamfanoni 8 da ke dauke da tarin rassa da kuma miliyoyin ma’aikata a yankunan biyu.
Alawadi da ke wannan batu yayin taron manema labarai da hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta shirya kan matakan da kamfanonin za su dauka a yaki da covid-19 dama shelanta irinin barnar da annobar ta haifar musu, ya ce zai iya kai akalla shekarar 2023 zuwa 2024 gabanin dawowar al’amuran sufurin yadda s uke.
A cewar shugabar hukumar ta WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti, wajibi ne kamfanonin sufurin su gindaya sharuddan karbar allurar rigakafi kan duk wanda ke bukatar bulaguro a sassan Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu