Isa ga babban shafi
kUDIN eCO

ECOWAS zata fara amfani da kudinta na bai-daya a 2027

Shugabannin kasashen Kungiyar Raya Tattalin Yammacin Africa ECOWAS/CEDEAO sun tsaida shawarar amfani da kudi bai daya a cikin shekara ta 2027.

Yanzu haka dai shugabannin kasashen na yammacin Afrika sun amince da kankamar shirin nan da shekarar 2020.
Yanzu haka dai shugabannin kasashen na yammacin Afrika sun amince da kankamar shirin nan da shekarar 2020. AFP Photo/ISSOUF SANOGO
Talla

Tun cikin watan Yunin shekarar 2019, Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta amince da matakin sanya sunan ECO ga takardar kudin bai-daya da kasashen yankin za su rika amfani da shi, daga watan Janairu na shekarar 2020, amma ta jingine saboda barkewar annobar Coronavirus.

Shugabannin kasashen na ECOWAS sun cimma matsayar ce, yayin taron da suka yi ranar 29 ga watan Yunin 2019 Abuja, babban birnin Najeriya.

Taron ya kuma baiwa cibiyar hada-hadar kudaden yammacin Afirka da kuma manyan bankunan kasashen yankin, umarnin soma aikin aiwatar da shirin fara amfani da kudin na bai-daya kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.