Isa ga babban shafi
Guinea-Muhalli

Guinea ta hana sara da sayar da itace a duk fadin kasar

Gwamnatin kasar Guinea ta haramta sara da kuma sayar da itatuwa a duk fadin kasar daga ranar 14 ga wannan wata na yuni lura da yadda matsalar sare itatuwa ke barazana ga muhalli da gandayen daji na kasar.

Garin Womey na kasar Guinée, a shekara ta 2015. (Photo d'illustration)
Garin Womey na kasar Guinée, a shekara ta 2015. (Photo d'illustration) The Washington Post via Getty Im - The Washington Post
Talla

Sanarwa daga ma’aikatar kare muhallli, ta ce daga yanzu an dakatar da bai wa kamfanoni da sauran masu sana’ar da sayar da itatuce lasisi, matakin da ake ganin cewa ba ya rasa nasaba da kama wasu manyan motoci dauke da itatuwan da aka sara a manyan gandayen dajin kasar biyu wato Farah da Mamou.

To sai dai Amadou Diakité shugaban wata kungiyar fafutukar kare muhalli mai suna Rénascedd, matakin ba shi ne zai kawo karshen wannan matsala ba lura da yadda dubban ‘yan kasar suka dogara da sana’ar sara da sayar da itace domin rayuwa, inda ya ce a maimakon haka kamata ya yi gwamnati ta samar da tsari na doka ga masu gudanar da sana’ar.

Alkalumma da ma’aikatar kare muhalli ta kasar Guinea ta fitar, na nuni da cewa a shekarar 1960, akwai gandayen dajin da fadinsu ya kai hekta milyan 14 a kasar, to sai dai a yanzu adadinsu bai wuce hekta dubu 700 ba saboda yadda ake saran itatuwa barkatai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.