Isa ga babban shafi
Faransa - Congo

Kotun Faransa ta kwace jirgin saman shugaban kasar Congo

Kotun daukaka kara ta Paris da ke Faransa ta tabbatar, kwace wani jirgin sama mallakin shugaban kasar Congo.

Wani jirgin sama kirar Falcon 7X, da aka adana a daukansu dake filin jiragen saman Bordeaux dake kasar Faransa
Wani jirgin sama kirar Falcon 7X, da aka adana a daukansu dake filin jiragen saman Bordeaux dake kasar Faransa AFP - MEHDI FEDOUACH
Talla

Wannan wani sabon koma baya ne ga Congo-Brazzaville a cikin wannan shari'a tsakanin shugabancin Jamhuriyar Congo da dan kasuwar dan asalin Anglo da Lebanon, Mohsen Hojeij, wanda ke bukatan kasar da ke Afirka ta biya shi bashin da yake binta tun  a shekarar 1992.

A farkon wannan watan hukumonin Faransa suka tsare jirgin kirar Falcon 7X, bisa bukatar kamfanin Commissimpex, wanda ke neman gwamnatin Congo ta biya shi bashin sama da Euro biliyan daya.

Diyya

Kotun daukaka kara ta Paris ta kuma umarci Jamhuriyar Congo da ta biya kamfanin Commissimpex euro dubu 50 a matsayin diyya.

Wannan shi ne karon farko da kutun Faransa ta tabbatar da yiwuwar kwace wani jirgin mallakin wata kasar waje.

Tuni hukumomin Congo suka ce  tsuguni bata kare ba, saboda zasu daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.