Congo ta nemi afuwa kan shelar yiwuwar sake aman wutar tsauni
Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta nemi afuwa bisa kuskuren da ta yi na yin shelar gargadin yiwuwar sake fuskantar aman wuta daga tsaunin Nyiragongo a ranar Juma’a.
Wallafawa ranar:
Gargadin na jiya dai ya firgita jama’a abinda ya sanya mutane kusan dubu 400 tserewa daga birnin Goma dake kusa da tsaunin mai aman wutar.
A makon da ya gabata tsaunin Nyiragongo ya yi aman wuta mai kunshe da narkaken dutsen da yayi sanadin mutuwar mutane akalla 12 duk da aikin kwashe dubban jama'ar da aka yi daga yankunan dake kusa da shi.
Yayin da kuma kididdigar da aka yi ta nuna sai da iftila’in aman wutar hade da narkakken dutsen ya lakume gidaje kimanin gidaje dubu 20 kafin ya tsaya a gaf da birnin Goma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu