Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

Shugaba da Firaministan Mali sun yi murabus gabanin ganawa da wakilcin ECOWAS

Majiyar Sojin Mali ta sanar da murabus din shugaba da Firaministan rikon kwarya na kasar yau Laraba gababin ganawa da masu shiga Tsakani na kungiyar ECOWAS bayan juyin Mulki irinsa na biyu cikin watanni 9.

Shugaban mulkin Soji na Mali Assimi Goita.
Shugaban mulkin Soji na Mali Assimi Goita. © Nipah Dennis / AFP
Talla

A kalaman babban mashawarcin shugaban sabuwar gwamnatin Sojin ta Mali Assimi Goita, Baba Cisse ya ce shugaba Bah Ndaw da Firaminista Moctor Ouane sun yi murabus gabanin ganawa da masu shiga tsakanin a wani bangaren na sharuddan sakinsu da tsarewar da ake musu tun bayan hambarar da gwamnatinsu.

Cikin kalaman na Baba Cisse, ya ce Sojin na gab da sakin hambararrun Firaministan da shugaban na Mali karkashin sasantawar masu shiga tsakanin na Ecowas bisa jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Tun a litinin din da ta gabata ne, Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Tarayyar Turai, AU da ECOWAS baya ga Amurka suka fara matsin lamba ga Malin wajen ganin ta kammala koma mulkin farar hula, matakin da ya kai ga sabon juyin mulkin karo na 2 a watanni 9.

Rahotanni sun ce Sojojin za su bai wa wakilan na ECOWAS damar ganawa da shugaban kasa da Firaministan da aka tsare bayan juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.