Isa ga babban shafi
Benin

Talon yasha rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adin shugabancin Benin

An rantsar da Shugaba Patrice Talon karo na biyu na shekaru biyar a kan shugabancin Benin, bayan sake zabensa a tsakiyar watan Afrilu da sama da kashi 86% na kuri’un da aka kada, a zaben da ba’a baiwa ‘yan adawa damar shiga ba.

Shugaban kasar Benin Patrice Talon yayin rantsuwar kama aiki a wani wa'adi na biyu ranar 23 ga watan Mayun 2021.
Shugaban kasar Benin Patrice Talon yayin rantsuwar kama aiki a wani wa'adi na biyu ranar 23 ga watan Mayun 2021. © YANICK FOLLY/AFP
Talla

Shugaban mai shekaru 63 ya yi alkawarin ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewar da aka fara tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2016. Don sake zabensa, ya iya dogaro da kyakkyawan tasirin tattalin arziki, musamman tare da gina tituna da cigaban makamashi da kayayyakin more rayuwa.

Shugaban kasar Benin Patrice Talon yayin rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adi na biyu na shugabancin kasar 23 ga watan Mayu 2021.
Shugaban kasar Benin Patrice Talon yayin rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adi na biyu na shugabancin kasar 23 ga watan Mayu 2021. © Presidence du Benin

Shugaban ya yi alkawarin cewa, "Wadannan matakan za su zama tushen arziki da ayyukan yi," wanda taken yakin neman zabensa ya kasance "ci gaba, mai dorewa kawai"

Benin ta kama hanyar zama na muklkin kama-karya

Tun bayan da aka zaɓe shi a shekarar 2016, Benin, wacce aka daɗe ana kallonta a matsayin abin koyi ga dimokiradiyya a Afirka ta Yamma, ta ɗauki salon mulkin kama-karya.

Shugaban kasar Benin Patrice Talon, watan Mayun 2021
Shugaban kasar Benin Patrice Talon, watan Mayun 2021 AFP - PIUS UTOMI EKPEI

Zaɓen shugaban ƙasa na watan Afrilu ya kasance irin wanda kasar bata taba gani ba, saboda an hana manyan 'yan adawa tsayawa takara, akasarinsu waɗanda ke gudun hijira, kuma manyan' yan adawa biyu, yayin da wasu mayan ‘yan takarar adawa yanzu haka suna tsare a kurkuku.

Wannan shine wa'adina na karshe - Talon

Bayan rantuwar kama aiki, shuga Patrice Talon yace ba shi da niyyar canza Kundin Tsarin Mulki domin ya sake tsayawa takara a karo na uku a shekarar 2026.

Kuna iya latsa alamar sautin domin sauraron abin da yake cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.