Isa ga babban shafi
Najeriya-Tsaro

Matsalar tsaro ce ta fi damu na-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar babban abin da ke damun sa shi ne matsalar tsaron da ta addabi kasar da zummar ganin ya kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaba Faustin-Archange Touadera na Afrika ta Tsakiya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaba Faustin-Archange Touadera na Afrika ta Tsakiya © Femi Adesina
Talla

Yayin da yake karbar bakwancin shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Toudera a fadarsa ta Abuja, Buhari ya ce, a koda yaushe abin da ya saka a gaba kenan, kuma shi ne dalilin da ya sa zai karbi bakwancin shugaban kasashen yankin Tafkin Chadi domin tattauna matsalolin da suka addabi yankin.

Buhari ya ce, batun janyo ruwa daga Tafkin Congo zuwa Tafkin Chadi na daga cikin batutuwan da ke dauke masa hankali, saboda muhimmancinsa ga sha’anin tsaro ganin yadda mutane sama da miliyan 30 suka dogara da shi domin rayuwa.

Shugaban Jamhuriyar Afirkar ya jajanta wa Najeriya kan rashin da ta yi na shugaban sojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da 'yan tawagarsa sakamakon hadarin jirgin sama.

Shugaba Toudera ya ce kasarsa na shirin sake gina rundunar sojin kasar, kuma yana bukatar Najeriya ta taimaka musu wajen ganin sun samu nasara.

Shugaban ya ce suna bukatar hulda kut-da-kut da Najeriya kuma dalilin ziyararsa kenan, inda ya bukaci yan kasuwar kasar da su je Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin zuba jari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.