Isa ga babban shafi
Afrika-Faransa

Tasirin taron tattalin arziki tsakanin shugabannin Afrika da Faransa

Yayin da ake kawo karshen taron shugabannin kasashen Afirka da na Faransa tare da wasu shugabannin hukumomin kudade na duniya, rahotanni sun bayyana cewar kwalliya ta fara biyan kudin sabulu sakamakon alkawuran da wasu hukumomi da kuma kasashe suka yi na taimakawa nahiyar wajen ganin ta shawo kan matsalolin tattalin arzikin da suka shafe ta sakamakon annobar corona.

Wani bangare na taron tattalin arziki tsakanin shugabannin Afrika da Faransa a Paris.
Wani bangare na taron tattalin arziki tsakanin shugabannin Afrika da Faransa a Paris. REUTERS - POOL
Talla

Daga cikin wadannan hukumomi akwai Bankin Duniya da hukumar bada lamuni ta duniya da Bankin raya kasashen Afirka da hukumar kasuwanci ta duniya da kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki da kuma wasu daidaikun kasashe.

Bankin duniya ya sanar da shirin zuba jarin Dala biliyan 2 wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar ta hanyar bai wa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa rance kai tsaye na Dala biliyan guda domin bunkasa harkokin kasuwancin su, yayin da kuma zai bada dala biliyan guda domin taimakawa manyan 'yan kasuwa wajen gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin sa da sauran kasashen duniya.

Shugaban Bankin da ke kula da sashen zuba jari Mokhtar Diop ya ce ta hanyar zuba jari ne kawai za a taimakawa kasashen Afirka wajen shawo kan matsalolin tattalin arzikin da ya dabaibaye ta.

Shima Yarima Mohammed bin Salman na Saudi Arabia ya bayyana shirin zuba jarin dala biliyan guda a wasu kasashen da ke Afirka a bangaren noma da hakar ma’adinai da kuma samar da makamashi.

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya ce bukatar su ita ce tara abinda ya kai dala miliyan 100 domin taimakawa kasashen na Afirka da ke cikin mawuyacin hali.

Shugaba Emmanuel Macron ya ce abin takaici ne yadda sauran kasashen duniya ke fafutukar farfado da tattalin arzikin su, amma aka yi watsi da Afirka wadda ta ke shan radadin illar da annobar corona ta haifar.

Daga cikin bukatar da wasu shugabannin Afirka suka gabatar wajen taron, musamman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ita ce na yafe bashin da ake bin wasu kasashen da ke Afirka domin farfado da tattalin arzikin su.

Kafin fara taron shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana yafewa Sudan bashin da kasar ke binta na kusan dala biliyan 5.

Ga alama kananan 'yan kasuwa ne suka fi jin radadin wannan matsala da annobar corona ta haifar, abinda ya sa Bankin duniya ya ce zai mayar da hankali wajen tallafa musu domin inganta harkokin kasuwancin su wadanda ke da matukar tasiri wajen habakar tattalin arzikin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.