Isa ga babban shafi
Najeriya-Chadi

Najeriya za ta taimaka wa Chadi wajen tabbatar da zaman lafiya-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta taimaka wa Chadi domin tabbatar da zaman lafiya da kuma komawar kasar kan tsarin doka da oda.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Shugaba Buhari ya dauki alkawarin ne a wannan juma’a lokacin da yake ganawa da Shugaban Majalisar Riko ta kasar Chadi Laftanal Janar Mahamat Idris Deby Itno wanda ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.

Sanarwar da mai taimaka wa shugaban Najeriya kan yada labarai Femi Adesina ya fitar jim kadan bayan wannan ganawa, ta ruwaito Buhari na cewa ‘’kasashen biyu na da abubuwan da suka hada su, wato al’adu da kuma makotaka’’, yana mai cewa ‘’Najeriya na sane da muhimmancin irin rawar da Chadi ta taka wajen yaki da ayyukan ta’addanci, kuma kasashen biyu za su ci gaba da wannan alaka a tsakaninsu’’.

Buhari ya bayyana tsohon shugaba Marshal Idris Deby Itno a matsayin “ amininsa sannan kuma cikakken aboki ga Najeriya da ba za a taba mantawa da irin rawar da ya taka don kare Najeriya ba.’’

Sanarwar ta kara da cewa Buhari zai bada gudunmuwar da ta dace don karfafa Hukumar Raya Tafkin Chadi (LCBC) da kuma jaddada goyon bayan ga Rundanar da

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.