Isa ga babban shafi
Chadi

An gabatar da sabuwar gwamnati da 'Yan adawa suka amince da ita a Chadi

Majalisar Mulkin soji dake kasar Chadi ta sanar da gwamnatin rikon kwarya wanda ake saran zata jagoranci kasar na watanni 18 zuwa zaben da za’ayi.

Shugaban majalisar sojin kasar Chadi kuma dan tsohon shugaban kasar Mahamat Idris Deby Itno
Shugaban majalisar sojin kasar Chadi kuma dan tsohon shugaban kasar Mahamat Idris Deby Itno Brahim ADJI Tchad Presidential Palace/AFP/File
Talla

Kakakin rundunar sojin Chadi Janar Azem Bermandoua Agouna ya bayyana sabuwar gwamnatin  mai dauke da ministoci da kuma mataimakan su 40 tare da kirkiro ma‘aikatar sasanta jama’a.

Sabuwar ma’aikatar zata yi aiki ne a karkashin jagorancin Acheikh ibn Oumar, daya daga cikin tsoffin 'Yan Tawayen kasar wanda ya zama mai baiwa shugaban kasa shawara a shekarar 2019.

Cikin wadanda aka nada har da shugaban 'Yan adawa Mahamat Ahmat Alhabo wanda zai zama ministan shari’a, amma ba‘ ambaci babban shugaban 'Yan adawar kasar Saleh Kebzabo ba.

Jogoran adawa bai cikin gwamnati

Kafin wannan lokaci Jam’iyyun adawa sun yi Allah wadai da sanarwar gwamnati na mayar da dimokiradiya Chadi a cikin watanni 18, to sai dai a hakin da ake ciki madugun jam'iyyun adawar kasar ya amince da sabuwar gwamnatin na rikon kwaryar da ya kunshi sojoji da fararen hula.

Bayanai na cewa wasu mutane biyu daga jam'iyyar jagoran adawar kasar Saleh Kebzabo na daga cikin mutane 40 da aka zaba amatsayin ministoci da mataimaka cikin sabon majalisar ministocin.

Janye dokar hana fitar dare

Majalisar Mulkin sojin  kasar Chadi ta sanar da janye dokar hana fitar da ta saka kwanaki 12 da suka gabata, bayan sanar da rasuwar shugaba Idris Deby Itno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.