Isa ga babban shafi
Chadi-Faransa

Faransa ta bayyana goyon baya ga sabon shugaban Chadi

A jiya Juma’a Chadi ta gudanar da jana’izar Idriss Deby Itno, jigo a yaki da ‘yan ta’addan yankin Sahel,  a yayin Faransa ta bayyana goyon baya ga dansa, wanda ya gaje shi, Mahamat Idriss Deby.

Mahamat Idriss Deby Itno, lsabon shugaban Chadi.
Mahamat Idriss Deby Itno, lsabon shugaban Chadi. © Tele Tchad via AP
Talla

Marigayi Idriss Deby,  wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasa ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu a wani gumurzu tsakanin sojojin gwamnati na ‘yan tawaye, kamar yadda sojin kasar suka sanar a ranar Talata.

Mutuwarsa ta girgiza abokansa na yankin Sahel da Faransa wacce ta yi musu mulkin mallaka, wadanda suka kwashe shekaru 9 su na yaki da ta’addancin da ya mamaye kasashe 3.

Rikicin ya lakume dubban rayuka, kana ya raba dubun dubata da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.