Isa ga babban shafi
Chadi - 'Yan Tawaye

Chadi ta sake fatattakan 'yan tawayen FACT dake neman hambare Deby

Sojojin Chadi sun yi ikirarin “tarwatsa” gungun ‘yan tawaye da suka kai hari arewacin kasar a ranar Lahadi, ranar zaben da shugaban kasa Idriss Déby Itno, da ke kan mulki na tsawon shekaru 30, ke tabbacin nasara.

Dakarun gwamnatin Chadi na sintiri kare birnin Djamena daga harin 'yan tawaye dake kokarin kifar da gwamnatin Deby, ranar Laraba 6 ga watan Fabrairun shekarar 2008.
Dakarun gwamnatin Chadi na sintiri kare birnin Djamena daga harin 'yan tawaye dake kokarin kifar da gwamnatin Deby, ranar Laraba 6 ga watan Fabrairun shekarar 2008. AP - Jerome Delay
Talla

Kakakin rundunar sojin kasar Azem Bermandoa ya sanar da haka maraicen jiya ta karfar talabijin din kasar, yana mai cewa "Jami'an tsaro sunyi nasarar murkushe gungun 'yan tawayen da suka kutsa kai zuwa arewacin Kanem, ba tare da bayyana adadin wadanda aka kashe ba.

A makon da ya gabata, kungiyar  ‘yan tawayen FACT wanda ta kunshi sojoji da ‘yan siyasan Chadi galibi kabilan Gorane, wata kabilar Sahara, ta kutsa kai cikin arewacin kasar, tare da ikirarin 'yantar da yankin na Tibesti" a arewacin kasar.

Chadi na fuskantar kutse 'yan tawaye jifa-jifa

Tibesti da kuma garuruwan kan iyaka da kasar Libya, na fuskantar hare-hare daga 'yan tawaye wadanda suke fafatawa da dakarun kasar a kai a kai.  A watan Fabrairun shekarar 2019, tawagar ‘yan tawaye da ta taso daga Libya tayi kokarin kifar da gwamnatin Shugaba Idriss Déby Itno, kafin hare-haren Faransa ya tarwatsa su, bisa bukatar N'Djamena.

A watan Fabrairun shekarar 2008, sai da wani harin tawaye ya isa ƙofar fadar shugaban ƙasa kafin a fatattake su tare da goyon bayan Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.