Isa ga babban shafi
Coronavirus-Afrika

Annobar Korona za ta jefa 'yan Afrika miliyan 30 cikin talauci - IMF

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF tayi gargadin cewar annobar Korona za ta jefa mutane sama da miliyan 30 cikin kangin talauci a yankin Afirka dake kudu da sahara, yayin da ta bukaci kasashe masu arziki da su taimakawa matalauta da maganin rigakafin cutar.

wata kasuwar saida kayayyakin masarufi a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe.
wata kasuwar saida kayayyakin masarufi a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe. AP - Tsvangirayi Mukwazhi
Talla

Hukumar bada lamunin tace wasu kasashen Afirka dake kokarin yiwa akalla kashi 60 na mutanen su rigakafi za su bukaci kashe karin kashi 50 na kudaden da suke warewa domin kula da lafiya.

Wata karamar kasuwa a birnin Legas dake Najeriya.
Wata karamar kasuwa a birnin Legas dake Najeriya. AP - Sunday Alamba

A shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasashen dake kudu da sahara ya samu koma baya na kashi 2, mafi muni da aka taba gani, sakamakon yadda annobar ta tilasta killace mutane cikin gidajen su da kuma rufe harkokin kasuwanci.

Sai dai a karshe hukumar ta IMF tayi hasashen cewar wadannan kasashe za su farfado nan da karshen shekara wajen samun habakar kusan kasha 3 da rabi, kamar yadda ake has ashen samu a kowanne sashe na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.