Isa ga babban shafi
Cote d’Ivoire-Gbagbo

ICC ta amince da sakin tsohon shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta Duniya ta amince da hukuncin sakin tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo da aka tuhuma da aikata laifuffukan yaki wajen tashin hankalin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasar.

Tsohon shugaban kasar Cote d'Voire Laurent Gbagbo.
Tsohon shugaban kasar Cote d'Voire Laurent Gbagbo. Jerry LAMPEN ANP/AFP/Archivos
Talla

Alkalan kotun da suka saurari daukaka karar da Fatou Bensouda ta yi bayan kotun ta yi watsi da karar da aka shirgar da farko sun ki amincewa da bukatar mai Gabatar da karar na sake matsayi akan hukuncin na da.

Mai shari’a Chile Eboe-Osuji ya sake tabbatar da hukuncin watsi da karar da aka yi a shekarar 2019, matakin da zai bai wa tsohon shugaban damar komawa gida.

An dai samu barkewar rikici a kasar Cote d’Ivoire ne bayan da shugaba Laurent Gbagbo yaki amincewa da kayen da ya sha a zaben shugaban kasa wanda hukumar zabe ta bayyana Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe.

Magoya bayan Gbagbo sun kaddamar da hare hare kan magoya bayan Ouattara, abinda ya yi sanadiyar rasa dimbin rayuka, kafin kawar da Gbagbo daga karagar mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.