Isa ga babban shafi
Somalia-Uganda

Sojojin Uganda sun yi ikirarin halaka mayakan Al Shebaab 189

Rundunar sojojin kasar Uganda tace dakarunta dake aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia sun kashe mayakan Al Shebaab akalla 189 a farmakin da suka kaiwa wani sansanonin kungiyar a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sojojin Uganda
Sojojin Uganda Arab News
Talla

Dakarun na Uganda sun kaiwa mayakan na Al Shebaa farmaki ne a kauyukan  Sigaale, Adimole da Kayitoye masu nisan akalla kilomita 100 daga Mogadishu babban birnin kasar.

Kawo yanzu dakarun wannzar da zaman lafiyar dake karkashin rundunar AMISOM ta kungiyar kasashen Afrika, sun shafe kalla shekaru 10 a Somalia, kuma Uganda ce kasa ta farko a Afrika da ta soma aikewa da sojojinta cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.