Isa ga babban shafi
ECOWAS

Shugabannin ECOWAS na taro karo na 58 a birnin Abuja

Shugabannin kasashen yammacin Afrika na kungiyar ECOWAS ko CEDAO na taro karo na 58 a Abuja, babban birnin Najeriya.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo yayin taron kungiyar ECOWAS karo na 58 a Abuja, ta kafar bidiyo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo yayin taron kungiyar ECOWAS karo na 58 a Abuja, ta kafar bidiyo. GhanaWeb
Talla

Taron da suka fara a yau Asabar ta kafar bidiyo, ya mayar da hankali wajen nazartar rahoton majalisar ministocin kasashen na ECOWAS kan batutuwan da suka shafi, tattalin arziki, tsaro, siyasa da wasu lamurran da dama.

Yayin jawabin bude taron, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo dake jagorantar kungiyar ta ECOWAS, yayi tsokaci kan tasirin annobar coronavirus kan tattalin arzikin yankin, tare da kiran daukar darasi kan kalubalen da aka fuskanta, sai kuma sha’anin tsaro musamman a Mali, Burkina Faso da Nijar, inda ya bukaci manyan kasashen duniya da su cika alkawarin bada tallafin dala biliyan guda don yakar ta’addanci a yankin Sahel.

Shugaban na Ghana ya kuma koka kan matsalar rashin tsaron dake karuwa ta ‘yan fashin teku a mashigin ruwan Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.