Isa ga babban shafi
Algeria

Kotun Algeria ta wanke dan uwan tsohon shugaban kasa Bouteflika

Kotun daukaka kara ta soji a Algeria ta wanke dan uwa ​​kuma tsohon mai ba da shawara ga hambararren shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika da wasu tsoffin shugabannin hukumar leken asiri biyu, wadanda aka yanke wa hukuncin shekaru 15 a kurkuku bisa laifin yin zagon kasa ga sojoji da kuma gwamnati.

Tsohon shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika da shugaban sojin kasar a lokacin sa
Tsohon shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika da shugaban sojin kasar a lokacin sa REUTERS/Ramzi Boudina
Talla

To sai dakuma a cewar wata majiyar shari'a, za a ci gaba da tsare Saïd Bouteflika a wani gidan yari har kafin kammala shari'a da ake masa kan wasu tuhuma daban da suka shafi cin hanci da rashawa a lokacin jagorancin dan uwansa da ya kwashe shekaru 20 yana mulkin kasar.

Baya ga Said Bouteflika, janarori Mohamed Mediène, da Athmane Tartag, da kuma wata 'yar gwagwarmayar Louisa Hanoune, wadanda aka yanke wa hukunci a wannan shari'ar, kotun daukaka karar ta wanke su.

A wani labarin kuma, ma’aikatar tsaron Algeria tabbatar da mutuwar sojojinta biyu da mahara masu ikirarin jihadi 4, bayan wani kazamin fafatawa a yankin Tipaza dake Yammacin Alger.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.