Isa ga babban shafi
Amurka-Mexico

Za mu sassanta da Mexico -Biden

Shugaban Amurika mai jiran gado Joe Biden ya tattauna ta wayar talho da Shugaban Mexico Andres Manuel Lopez Obrador.shugabanin biyu sun tattauna dangane da tsaikon da suke fuskanta kan iyakokin kasashen Amurika da Mexico .

Andres Manuel Lopez Obrador  shugaban kasar Mexico
Andres Manuel Lopez Obrador shugaban kasar Mexico REUTERS/Edgard Garrido
Talla

A daya geffen Shugabanin biyu sun mayar da hankali dangane da hanyoyin da suka dace Mexico da Amurika su yi amfani da su don yakar cutar Covid 19 da kuma batun kasuwanci dake tsakanin su.

Joe Biden zabbaben shugaban Amurika na fatan sake farfado da dangantakar hulda dake tsakanin kasar sa Amurika da Mexico.

Tsawon lokacin da Shugaba mai baring ado Donald Trump ya jagoranci shugabancin Amurika, Mexico ta kasance tamkar kasar da ya dace a hana yan kasar shiga Amurika,lamarin da ya sa Shugaba Trump gina Katanga a kan iyakar kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.