Isa ga babban shafi
Mozambique

Ta'addanci: MDD na neman dala miliyan 254 don tallafawa Mozambique

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar Dala miliyan 254 domin taimakawa daruruwan mutanen da Yan tawayen masu ikrarin jihadi suka raba da muhallansu a kasar Mozambique.

Wasu 'yan gudun hijira a Mozambique da matsalar tsaro ta raba da muhallansu
Wasu 'yan gudun hijira a Mozambique da matsalar tsaro ta raba da muhallansu Médecins Sans Frontières
Talla

Majalisar tace hare haren ‘yan tawayen ya sanya dubban mutanen barin gidajensu ba tare da daukar komai ba, banda kayan jikinsu, yayin da tayi gargadin cewar yawansu na iya kaiwa sama da miliyan guda a shekara mai zuwa.

Ita dai wannan kungiya ta kaddamar da hare hare ne tun daga shekarar 2017 a birnin Mocimboa da Praia dake da tashar jiragen ruwa, kumą kawo yanzu ta kashe mutane sama da dubu 2 da 300.

A cikin wannan mako kungiyar kasashen Turai EU tayi alkawarin taimakawa kasar wajen murkushe ‘yan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.