Isa ga babban shafi
Afirka

Sama da mutane miliyan 2 sun harbu da korona a Afirka

Yayinda kasashen duniya ke ci gaba da hakilon neman maganin cutar Coronavirus da ya buwayi kasashen duniya alkaluman mutanen da suka harbu da wannan cuta a nahiyar Afirka sun zarce miliyan biyu.

Ma'aikatan kiwon lafiya dake kula da annobar korona a Afirka ta Kudu
Ma'aikatan kiwon lafiya dake kula da annobar korona a Afirka ta Kudu Michele Spatari/AFP/Getty Images
Talla

Bayanai daga Ofishin dake sa ido da rigakafin yaduwar cutuka a nahiyar Afirka dake Nairobi na kasar Kenya, na cewa nahiyar mai jimillar kasashe 54 ta kuma sami mamata sakamakon kamuwa da wannan cuta da suka kai dubu 48.

Cibiyar ta ce nahiyar Africa mai jimillan mutane Biliyan daya, da miliyan dari uku, na fuskantar kalubalen yin takatsantsan da sharuddan da aka gindaya don hana bazuwar cutar.

A farkon wannan mako da muke ciki Daraktan cibiyar ya bayyana fargaba saboda yadda a kasashen nahiyar wasu mutane suka yi watsi da matakin sanya takunkumin rufe baki da hanci don kada su harbu da wannan cuta.

Ganin yadda duniya ta bada karfi wajen samo maganin wannan cuta ayanzu, yasa jamian lafiya ke ganin dacewar tsaurara matakan kariya daga cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.