'Yan tawayen Tigray sun yi barazanar kaiwa Eritrea farmaki
Jam’iyyar TPLF mai mulkin yankin Tigray da ta bijirewa gwamnatin Habasha, ta dauki alhakin jerin hare-haren makaman roka da ta aka kaiwa wasu filayen jiragen sama dake gaf da yankin.
Wallafawa ranar:
Daya daga cikin jagororin jam’iyyar ta TPLF Getachew Reda ya ce sun kai farmakin ne da zummar dakile shirye-shiryen dakarun Habasha na kai musu farmaki daga sansanoninsu dake yankunan Massawa da Asmara a kasar Eritrea dake makwabtaka da yankin na Tigray a kasar ta Habasha.
‘Yan tawayen na Tigray sun kuma yi barazanar kaddamar da hare-hare kan wasu yankunan kasar Eritrea da suka yi iyaka da ita, muddin ta cigaba da baiwa dakarun Habasha damar kafa sansanoninsu a kasar.
A karshen makon nan majalisar dinkin duniya ta yi gargadin yiwuwar tafka laifukan yaki a yankin Tigray na Habasha, inda a yanzu haka ake gwabza fada tsakanin sojojin kasar da kuma ‘yan tawayen da ke marawa jam’iyyar TPLF mai mulkin yankin da ta bijirewa gwamnati.
A makon jiya Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya bada umarnin kaddamar da farmakin soji kan mayakan sa kan na Tigray, bayada ya tuhumi shugabannin yankin da yunkurin haifar tashin hankali a kasar, ta hanyar daukar nauyin horas da mayaka tare da basu makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu