Isa ga babban shafi

Jiga jigan 'yan siyasar Amurka sun taya Biden murna

Jiga jigan 'yan siyasar Amurka da fitattaun 'yan kasar na ci gaba da aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Joe Biden da Sanata Kamala Harris sakamakon gagarumar nasarar da suka samu wajen kawar da shugaba Donald Trump daga karagar mulki.

Barack Obama, tsohon shugaban Amurka, kuma daya daga cikin wadanda suka taya Biden murna.
Barack Obama, tsohon shugaban Amurka, kuma daya daga cikin wadanda suka taya Biden murna. AP Photo/John Raoux
Talla

Daga cikin tsoffin shugabannin da suka aike da sakon fatar alheri akwai tsoffin shugabannin kasar irin su Bill Clinton da Barack Obama da Jimmy Carter.

Carter ya ce shi da uwargidansa Rosalynn na taya Biden da Kamala Harris murnar nasarar da suka samu bayan tsaftacacen yakin neman zabe, kuma suna fatar ganin sauye sauye masu tasiri a jagorancin su.

Obama ya ce wannan zabe mai dimbin tarihi ya nuna yadda aka samu Amurkawa masu kada kuri’u sabanin yadda aka saba, kuma muddin aka kidaya kowacce kuri’a Biden da Harris zasu kafa tarihi a kasar.

Clinton ya ce Amurka tayi magana, kuma dimokiradiya ta samu nasara. Yanzu an samu zababben shugaban kasa da mataimakiyar sa wadanda za suyi aiki tare wajen hada kan kasa.

Shugabar Majalisar wakilai Nancy Pelosi ta bayyana yau a matsayin wata sabuwar rana mai cike da fata ga Amurka inda Amurkawa sama da miliyan 75 suka kada kuri’a ga zababben shugaban kasa Biden wanda ya kafa tarihi da kuma mikawa Jam’iyyar Democrat shugabanci.

Sanata Mitt Romney na Jam’iyyar Donald Trump yace shi da uwargidan sa Ann na aikewa da sakon taya murna ga zababben shugaban kasa da mataimakiyar sa Kamala Harris, kuma suna sane da cewar dukkan su mutanen kirki ne kuma abin koyi.

Sauran wadanda suka aike da sako sun hada da Jeb Bush da Hillary Clinton da Sanata Bernie Sanders da Elizabeth Warren da Newt Gingrich da LeBron James da kuma Kim Kardashian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.