Yayinda ake ci gaba da kada kuri’a a zaben shugabancin kasar Amurka, da dama daga cikin kasashen Duniya sun zura ido a kai.Abdoulaye Issa ya samu tattaunawa da Abba Sediq, Dan Jarida mai sharhi kuma manazarci a lamuran da suka jibanci halaya da zamantakewar dan Adam a Afrika, wanda ya duba mana irin yada jama’a suka raja’a wajen kada kuri’a da kuma abinda kan iya biyo bayan zaben ta fuskar diflomasiya da siyasa da kasashen Duniya..
Miliyoyin Amurkawa ke kada kuri’u yau a zaben na Amurka wanda tuni ya dauke hankalin kasashen duniya wadanda suka zuba ido domin ganin wanda zai samu nasara tsakanin shugaba Donald Trump da ya kwashe shekaru 4 a karagar mulki da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.
Muhimmancin zaben Amurka ta fuskar diflomasiya da kasashen Duniya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu