Isa ga babban shafi
Habasha

'Yan Oromo na bikin shigowar kakar bana a Habasha

Dubban al’ummar Habasha daga kabilar Oromo wadda ita ce mafi girma a kasar, na gudanar da wani gagarumin bikin nuna godiya a birnin Bishoftu karkashin cikakken tsaro bayan hukumomin kasar sun ce, sun kwace makamai tare da dakile wani hari da aka yi nufin kaddamarwa kan jama’ar da ke halartar bikin na kwanaki biyu.

Bikin Ireechaa na bana an gudanar da shi cikin fargaba
Bikin Ireechaa na bana an gudanar da shi cikin fargaba YONAS TADESSE / AFP
Talla

Wannan biki da ake yi wa lakabi da Irreecha ya yi kaurin suna, ganin yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula a yayin gudanar da shi a duk shekara, yayin da a wannan karo fargaba ta tsananta saboda kisan da aka yi wa wani shahararren mawaki a kasar, yayin da aka cafke jiga-jigan ‘yan saiyasar kabilar ta Oromo.

Ana gudanar da bikin ne don nuna godiya ga wucewar damuwa da kuma kintsawa shiga sabuwar kakar girbe albarkatun gona.

A bana dai mutane kalilan ne suka halarci gagarumin bikin saboda fargabar rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.